Thursday, 30 November 2017

Yadda Na Kama Mai Dakina Tana Turawa Samarinta Hotunan Tsiraicinta

Jaridar Pulse.ng ta rawaito labarin wani matashin magidanci dan shekaru 38 da haihuwa kuma mazauninAbuja kan yadda ya yi kicibis da tattaunawar mai dakinsa da wasu maza biyu ta kafar WhatsApp, inda mai dakin tasa ke tattaunawa cikin shauki da mazajen tare kuma da hotunan tsiraicinta sama da guda 20 da turawa mazajen guda biyu

Wannan matashi da Pulse ta bayyana sunansa da Jonathan ya bayyana cewa matarsa ta shekaru 8 kuma uwar ‘ya’yansa mai suna Valerie na cin amanarsa sakamakon nisa da ke tsakaninsu

Lamarin dai ya fara ne tun daga lokacin da aka dauke Jonathan daga ofishinsu na Legas zuwa Abuja. Amma a maimakon Jonathan ya dauke iyalinsa gaba daya zuwa Abuja, sai ya zabi ya koma Abuja shi kadai saboda aikin da mai dakinsa ke yi da kuma makaranta da ‘ya’yan nasu suka fara zuwa
Jonathan ya ce, duk a wannan lokaci ban taba barin matata da bukatata ba, domin dai ian zuwa Legas a kai-a kai, kuma bana barin Legas sai na tabbata na fanshe mata kwanakin da na dauka bana nan ta hanyar biya mata bukatr aure gamsasshe
Dubun matata ya cika ne a lokacin da na zo hutun cikar Nijeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai (1 ga watan Oktoba, 2017) sai na yi rashin dace na’ura mai kwakwalwata ta hannu ta samu matsala kuma a lokacin wayata babu data kuma ga shi ina da bukatar aika email zuwa ga mai gidana
Bayan na aika email din ne kawai sai wani abin ya ce bari na bude WhatsApp dinta, kuma ban yi hakan da niyyar bincike ba. Ko da budewa ta sai na yi kicibus da wani suna da ban san shi ba, hakan ya sa na bude don ganin ko wanene tunda na san ‘yan uwanta maza da abokan aikinta
Budewa ke da wuya sai na ga tattaunawarsu da alamar alakantuwa da shakuwa. Hakan ya sa na ci gaba da duda hirar tasu har na ga inda suke bayyanawa juna yadda suka ji dadin juna a haduwansu na baya tare da fatan sake haduwa nan ba da dadewa ba
Na ci gaba da dubawa, sai ga hotunan farjin nonuwan mata da farjinta ta tura wa mutaumin. Nan fa na shiga bincike, inda na sake samun wani namijin dai da take aikata irin wancan abu da ta ke yi da na farkon
Ai kuwa ban san lokacin da na fara zub da hawaye ba cike da takaici. Na zauna tsawon shekaru biyu a Abuja (daga shekarar 2015 zuwa 2017) ban taba cin amanar mai dakina ba saboda kaunar da na ke yi mata
Ina cikin kukan ne fa matata ta shigo ta ganni rike da wayarta, sai ta koma da gudu ta shiga dakin baki ta rufe kofa

Nan take ni kuma na yi wanka na shirya yarana na dauke sai gidan yayata. Na umarce ta da ta ajiye min su zuwa lokacin da zan warware matsalata
Daga nan na koma gida na tattara ya nawa ya nawa na koma Abuja kuma har zuwa yanzu ban kara taka kafata zuwa Legas ba. Sai dai mai dakina na ta aiko min da sakon neman yafiya, tare da fada min cewa wai kadaici da sharrin shaidan ne ya jefa ta cikin halin da ta tsinci kanta
Bana jin zan iya yafe mata, amma ina tunanin halin da ‘ya’yanmu za su shiga in na saketa

Source:- Alummata.Com

No comments:

Post a Comment