Thursday, 30 November 2017

Yadda Na Samowa Kanina Matar Aure A Shafin Twitter: Muhammad Baba


Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Muhammad Baba ya bayyana yadda ya samawa kanin shi mata ta shafin na Twitter bayan ya wallafa sanarwa a watan Maris din shekarar nan.
Baba dai ya rubuta cewa kanin shi na bukatar mata ‘yar misalin shekaru 24 zuwa 26, doguwa, wacce ta ke motsa jikinta, ta iya girki kuma ta ke da digiri.
Sannan ya bayyana cewa kanin shi na daukan sama da Naira dubu 200 a wata.
A cewar Baba, an yi ta caccakar shi a lokacin, amma wata baiwar Allah ta ga sakon na shi ta amsa, kuma yau ga shi nan ta na shirin aure da dan uwan na shi.
Ya ce za a yi auren a ranar 23 ga watan Gobe.

No comments:

Post a Comment