Wednesday, 7 March 2018

Fim din Basma ne ya fi Bani Wahala - InJi Fati Shu'uma

Shaharariyyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Fati Abubakar wacce aka fi sani da Fati Shu’uma ta bayyana fim din ‘Basma’ a matsayin fin din da ya fi ba ta wahala. 


A cewar jarumar fim din Basma yayi matukar wahalar da ita saboda yarinyar da aka hada ta fim din da ita wacce ta wuce shekaru bakwai ba a duniya. 

Sannan kuma wannan fim din ya kasance fim din yarinyar na farko, saboda haka id aka kai wa yarinyar mangari ko naushi sai ta ji kamar da gaske ne harma ta tsaorata. 

Fati tace wannan ya sa sai da aka ta sake daukar fim din sau da dama kafin a kammala shi.

Ta ce "yarinyar da aka hada ni fim da ita, wacce ba ta wuce shekara bakwai ba, shi ne fim dinta na farko, don haka idan na kai mata mangari ko naushi takan ji kamar da gaske ne sai ta tsorata. 

"Don haka sai da aka rika sake daukar fim din sau da dama kafin a gama shi". 

No comments:

Post a Comment