Monday, 4 December 2017

illolin Fifita Msta Akan Mahaifiya


Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili mai albarka mai fadakarwa, ilimantarwa da kuma a wani lokaci yake nishadantarwa.  A yau zan tabo wani muhimmin batu ne na yadda wadansu mutane maza da mata suke musgunawa iyayensu saboda sun auri wani ko wata saboda wasu dalilai na kashin kansu da hakan ya ci karo da koyarwar addinin Islama.
Abin takaici ne yadda za ka tarar wasu ke fifita matansu na aure a kan iyayen da suka haife su wai saboda “tsabagen son” da suke yi wa matan nasu.
A hakikanin gaskiya hakan na faruwa a wannan zamani a mafi yawa daga cikin gidajen aure.  A addinance dai an nuna bayan yi wa Allah da ManzonSa, Annabi Muhammad (SAW) biyayya, babu wani abu da ya wuce yi wa iyaye biyayya in dai biyayyar ba ta saba wa addinin Islama ba.
A gaskiya irin abin da ke faruwa a mafi yawa daga gidajen aure kenan ciki har da al’ummar Hausawa. Sai ka tarar ba kunya, ba tsoron Allah namiji yana fifita matarsa a kan iyayensa.  Haka ma a wasu lokuta ana samun irin haka a bangaren mace inda wasu ke fifita mazajensu fiye da iyayensu.  Amma ba kasafai ake samun irin haka a tsakanin mata ba, don da wuya ka iske mace tana wulakanta iyayenta a kan namiji akasin yadda namiji yake wulakanta nasa iyayen a kan mace.
Kafin ka samu gidan da mace take fifita mijinta a kan iyayenta sai ka sha wahala, amma abu ne mafi sauki ka samu labarin yadda wasu maza ke fifita matansu fiye da iyayensu, wannan kuma ba karamin kuskure ba ne.
Kan haka ne nake son janyo hankalin maza ko mata masu aikata irin haka da su ji tsoron Allah, don babu abin da ya wuce yi wa iyaye biyayya da kuma kyautata musu, don duk irin takamarka su ne suka haife ka, da ba su yi sanadiyyar zuwanka duniya ba, da ba ka zama abin da ka zama a yau da kake tinkaho kana dagawa ba. 
Kenan duk wanda ya saba wa iyayensa in dai a kan tafarkin addinin Islama ne, to tamkar ya saba wa Allah da MansonSa ne, don wajibi ne yi wa iyaye biyayya, ba zabi ne ba.
Hasalima, addinin Islama ya nuna tilas ne da ya yi wa iyayensa biyayya ko da sun kasance ba addininsu daya ba, sai dai ba zai bi umarin da suka ba shi ba ne in ya saba wa addinin Islama amma duk da haka tilas ne ya rika kyautata musu ta hanyar da ta fi dacewa da kuma bin su cikin lalama, ba yin fito-na-fito ba.
A kan haka ne zan bayar da wannan labari da ya faru da wasu ’ya’yan wata mata, wa da kanwa inda suka wulakanta mahaifiyarsu don ya zama darasi ga masu neman aikata irin haka.  Labarin dai ya faru ne a daya daga cikin jihohin kasar nan  sai dai kamar kullum ba zan so na ambaci Jihar da abin ya faru ba saboda wasu dalilai.
A wani gari ne wata mata tana da yara biyu, wa da kanwa tun suna kanana mahaifinsu watau mijinta ya rasu. Haka mahaifiyar ta ci gaba da daukar dawainiyar ’ya’yanta ba tare da nuna gajiyawa ba, ta hanyar samar musu da abinci da biya musu kudin makaranta da sauran bukatu na yau da kullum.  Har sai da ta kai ga ’ya’yan nata sun girma.  Bayan sun kammala karatun sakandare sai ta yi wa macen aure yayin da namijin kuma ya ci gaba da yin karatu a wata Jami’a.
Bayan dan ya kammala karatu kuma ya yi bautar kasa (NYSC) sai Allah Ya taimaka ya samu aiki da wani banki, inda aka ba shi babban matsayi.
Cikin kankanen lokaci, dan ya samu abin duniya inda ya sayi katafaren gida da mota sannan ya dauki mahaifiyarsa suka koma gidan suka ci gaba da zama.  Da ma tun farko suna zaune ne a gidan haya, don haka yanzu da daula ta samu sai ya mayar da ita gidan da ya saya suka ci gaba da zama tare.
Ita kuwa kanwarsa, bayan ta kammala karatun sakandare sai uwar ta yi mata aure da wani matashi mai rufin asiri, inda suka ci gaba da zaman aure cikin lumana da kwanciyar hankali.  Sannan ita ma mijinta yana da niyyar ta ci gaba da yin karatun boko mai zurfi idan abubuwa duka daidaita.
Shi kuma danta sai uwar ta nemo masa auren wata makwabciyarsu da ta amince da dabi’unta, inda aka hada su aure.  Amarya ta tare a gidan dan tare da mahaifiyarsa.  danta da amaryarsa suna bangarensu yayin da uwarsu kuma take bangarenta.
 Da tafiya ta fara nisa ne sai dan ya fara canzawa amaryar tasa, inda ta rika kai kukanta ga mahaifiyarsa, ita kuma tana yi masa fada don ya gyara.  Ashe hakan bai yi wa dan dadi ba, inda ya bari wata rana mahaifiyar ta fita unguwa shi kuma sai ya saki matar, saki uku ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.  Bayan mahaifiyarsa ta koma gida ne sai ta iske danta ya saki matarsa, da ta nemi dalilinsa na yin haka ya kasa yi mata wani bayani mai gamsarwa.  Mahaifiyar ta yi matukar bakin ciki a kan matakin da danta ya dauka na sakin wannan mata tasa mai natsuwa da hankali har saki uku a take ba tare da ya sanar da ita ba.  Haka ta ci gaba da zama cikin bakin ciki da takaici.  Da danta ya lura ta shiga damuwa, sai ya rika yin baya-baya da ita. A da yakan ziyarci bangarenta a kodayaushe amma sai ya koma jefi-jefi.
Ashe ba ta sani ba ya hadu da wata yarinya ce a waje da ta hure masa kunne.  Yarinya ce wacce ba ta da tarbiyya, hasalima sun yi haduwa ne irin haduwar bariki.  Labarin ya nuna suna aiki ne a banki daya, da hakan ta sa suka shaku da juna.
Mu Kwana nan
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883
Daga: Jaridar Aminiya

No comments:

Post a Comment