Monday, 4 December 2017

Jaruma NaFisat Abdullahi .. Ta Bayyana AlaKar Dake Tsakaninta Da Rahma Sadau


Shaharariyar jarumar finafinan Hausa Nafisa Abdullahi ta fito tayi bayanin ainihin alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami.
Jarumar dai tayi wannan karin haske a wata hira da aka yi da ita a Weekly Trust jim-kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita zaune take lafiya da kowane abokin sana’arta.
A lokacin da aka tambaye ta Nafisa Abdullahi ko da gaske ne basa ko ga-maciji tsakanin ta da Rahama Sadau, sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani sabani a tsakanin su yanzu.
Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma dukkan su suna yin aiki ne a karkashin kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace kuma suna fada da junan su.

No comments:

Post a Comment