Tuesday, 26 December 2017

Jerin Jaruman Kannywood Da Akesa Ran Zasu Mamaye Gurbi A 2018


Manyan gobe da zasu zama idon jama'a a masana'antar nishadantarwa ta kannywood cikin 2018


Hakika masana'antar Kannywood ta samu farin jini da daukaka sanadiyar ire-iren damar da take baiwa masu basirar yin waka ko fitowa a wasan kwaikwayo.


Wannan dandalin ta cigaba da bunkasa martaban arewan ta hanyar wasanni don nishadantarwa da fadakar da jama'a da labarurruka masu kayatarwa.

A cikin shekara ta 2017 Kannywood ta samu canji ko kuma ince ta fara sauya yadda aka saba ganin fina-finan ta sanadiyar kaddamar da tsarin Box office wanda zai taimakawa wajen haska fina-finai a sinimomi da gidajen kallo.

Hakazalika masu ruwa da tsaki na masana'antar sun gyara fuskar yadda suke shirya fina-finai inda a halin yanzu suna takama da kayan aikin fasahar zamani wajen shirya fim.

A 2017 kannywood ta samu wasu sabbin jarumai tare da tsoffin jarumai matasa wadanda tauraron su ke haskawa
Ga wasu cikin su muna iya cewa sun shigo masana'antar da kafar dama yayin da sauran ke jajircewa wajen bayyana basirar su bainar jama'a.
Ga jerin jarumai wanda muke ganin cikin 2018 gwanintar su da kuma nuna fasahar su zai janyo haske ga tauraron su a masana'antar.

Munyi masu lakabi da "Manyan Gobe";

1. Maryam Yahaya


Bana wannan jaruma tana sahun gaba cikin jarumai da tauraron su ya haska.

Bayan fitowar ta shirin "Mansoor" ta cigaba da nuna mana irin basirar dake tattare da ita wanda suma masu shiryawa fina-finai suka shaida hakan har ma suke ta haska ta a fina-finai daban daban.

2. Rashida Lobbo


Bana dai wannan jarumar ta samu kyautar city people awards a jihar legas bisa ga rawan da ta taka a masana'antar Kannywood.

3. Amal Umar


Amal tana cikin yan wasa da suka yi fice acikin shirin MTV "shuga" wanda ake yi cikin harsheb turanci. Banda haka jarumar ta fito a fina-finai da dama na masana'antar kannywood.

4. Umar M.Sheriff


Fitaccen mawaki Umar M.Sheriff ya gwada iyawan shi fitowaer shi a cikin "mansoor" a matsayin jarumi kuma da alama ya ji dadin hakan kuma zai cigaba da damawa a cikin harkar.

5. Halima Ibrahim


Jarumar ta fito a cikin shirin "Rabu da Maza" tare da fitaccen jarumi Sadiq Sani Sadiq da kuma jaruma Amal Umar

6. Garzali Miko


Shima dai wannan mawaki yana tafarkin sauya sheka zuwa fannin fim.

7. Ahmad Illiyas Tantiri


Ahmad daya daga cikin yaran babban direkta kuma mai shirya fim ne watau Abdulmumin Illiyas Tantiri.
Yana daya daga cikin yara dake kokartawa a farfajiyar fim.

Source Fulse.ng

No comments:

Post a Comment