Saturday, 2 December 2017

Saukin kai gare ni - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi


Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Nafisa Abdullahi hakika babbar jaruma ce da ta shafe shekaru da dama a masana'antar tare kuma da lashe kyaututtuka masu tarin yawa daga ciki da kuma wajen kasar nan. 

HAUSAMINI.com dai ta samu cewa jarumar tayi wannan tsokacin ne a yayin wata fira da tayi da majiyar mu ta Weekly trust jim kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan. 

A cewar ta da wannan zargin da ake yi mata dai sharri ne amma akwai lokutan da mutum yana wasu harkokin gaban sa ne ko kuma abubuwan duniya sun ishe shi to idan bai ba masoyan nashi cikakkiyar kulawa ba sai a dauka ko haka yake. 

Daga karshe ne sai kuma ta kara tabbatar wa da magoya bayan ta cikakkiyar kaunar ta agare su tare da shan alwashin cigaba da kayatar da su a cikin fina-finan ta. 

No comments:

Post a Comment