Wednesday, 3 January 2018

Babban Burina Shine Nayi Aure Na Zama Uwa - Inji Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar nan dake yin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana wa duniya babban burin ta a rayuwa a halin yanzu. 

Jarumar dai ta bayyana cewa ita yanzu bata da burin da ya wuce tayi aure sannan ta kuma haihu ta zama uwa. 

Jarumar dai ta bayyana hakan ne lokacin da take bayar da ansa ga masoyan ta da ta damar yi mata tambaya a shafin ta na dandalin zumuntar zamani na Instagram a kwanan baya. 

Ta amsa cewa “Ali Nuhu.” 

Me ta fi jin tsoro a duniya? 

Ta ce “mutuwa.” 

Yaushe za ta yi aure? 

Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba. 

Shin za ta iya daina fim? 

Ta ce “a’a.” 

Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa 

Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.” 

Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta Ta ce fim din turanci na 

“Sons of the Caliphate” 

No comments:

Post a Comment