Friday, 9 March 2018

Buruka na sun cika, saura aure kawai yanzu - Inji Aisha Tsamiya

Fitacciyar jarumar wasan Hausa ta fina-finan Kannywood watau Aisha Aliyu da aka fi sani da Aisha Tsamiya ta bayyana cewa yanzu kam burikan ta a rayuwa duka sun cika saura aure kawai 

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da ta yi da majiyar mu a karshen mako inda ta bayyana cewa dama can burin da take da shi shine karatu wanda kuma tuni tayi nisa a cikin sa. 

HausaMini.com ta kuma samu daga jarumar bugu da kari cewar ta bayyana rade-raden da ake yi na cewa 'yan fim basa son aure a matsayin labarin kanzon kurege da tace bai da tushe balle makama. 

Jamrumar ta bayyana cewa silar aure ne ya sa suka zo duniya don haka kuwa ba yadda za'ayi ta guji aure sannan kuma daman cikar darajar mace yanzu a duniya shine a dakin mijin ta. 

No comments:

Post a Comment