Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Adam Zango Yana Shirya Sabon Fim Tare Da Tsohuwar matarsa


HausaMini


Tsohuwar jaruma Maryam Abdullahi wadda akafi sani da Maryam Ab Yola tsohuwar matar Jarumi Adam A Zango ta uku wadda suka rabu a shekarun da suka wuce.  Jaruman dai kafin aurensu sunyi finafinai Irinsu NASS da ALKAWARI tare.

Zango da Maryam sunyi aure a 2013 bayan gama daukar film din NASS, An daura auren ne a Lugbe wata Unguwa a garin Abuja. Sun rabu bayan ta haifa masa yaro daya.


Wani abin mamaki shine Maryam yanzu ta dawo film ta hanyar tsohon mijinta inda ya sakata acikin wani shirin film Dinshi mai suna RAMAKON GAYYA wanda Bello Muhammad Bello yake bada Umarni.

Yanzu haka dai angama daukar kashin farko na film din,  zuwa nan gaba za'a cigaba.Source-: FimHausa

Share this


0 comments:

Post a Comment

HausaMini.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By HausaMeDia