Friday, 9 March 2018

Karanta Labarin Macen DaTa Haihu Ba Tare Da TaSan Tana Da Ciki Ba


Abin mamaki ba ya karewa, Allah mai yadda Ya so, wata budurwa ta haifi santaleliyar jinjira ba tare da ita kanta uwar ta san tana da cikinta ba, har sai lokacin da ta garzaya asibiti domin neman taimako a kan ciwon da ta ji cikinta yana yi da kuma jinin da ta ga yana zuban mata haka siddan ba gaira ba sabar, a zaton ta.

Charlotte Thomson, ‘yar shekaru 21 da haihuwa, wacce ke da zama a Anguwar Tyne, da ke can birnin Newcastle, ta kasar Ingila, har ya zuwa ranar da ta garzaya asibitin, ba ta daina ganin jinin ta na al’ada ba a duk wata kamar kowace mata marar juna biyu. Sannan kuma ba ta taba yunkurin canza tufafin da take sanyawa ba domin tunanin ko tana da juna biyu.

Isar ta asibitin ke da wuya, ta shaidawa likita ciwon cikin da ke damunta da kuma jinin da ya barke mata haka siddan, dubawan da likita zai yi, sai ya budi baki ya ce mata, “Ai haihuwar ce ta zo.” Charlotte Thomson, ta ce, na kadu, kuma na gigita da jin wannan jawabin da ya fito daga bakin likitan, domin ni har ranar da na zo asibitin ban fasa ganin al’ada ta ba a duk wata, ban kuma taba jin wata alama a jikina na alamun akwai wani abu a cikin ciki na ba.

Kai, ban dai sakankance da gaskiyar jawabin likitan ba, har sai da na ga da gaske, an kai ni dakin haihuwa, an kuma kwantar da ni, kuma wai sai ga haihuwar da gaske, inda kasa da awannin biyu kacal da zuwa na asibitin, sai ga shi na haifo santaleliyar jaririya cikin koshin lafiyarta. Lamarin ya ba ni tsoro matuka, na kuma gigita, sai na rika ganin abin kamar a mafarki, a ce wai na haihu ba tare da jin wani alami ba.

Charlotte Thomson, ta ce, tana da tabbacin tsohon saurayinta ne ya yi mata cikin, ta kuma ce, ta dai yi la’akari da yadda nauyinta ya dan karu kadan da laba uku, a lokacin da take da cikin, amma sam ba ta kawo cewa ciki ne ba, kasantuwar ta kullum a gidajen rawa da kuma, ‘Party.’ “Ni na yi zaton yanayin fitan da nake yi ne barkatai, in ci banza, in ci wofi, shi ne dalilin dan nauyin da na kara.”

“Ni na yi zaton yanayin fitan da nake yi ne barkatai, in ci banza, in ci wofi, shi ne dalilin dan nauyin da na kara.” 

A cikin watan Disamba na shekarar 2015 ne, kawai watarana da misalin karfe 2:30 na dare, sai na farka na ji alamun jini na fitar mani, nan na nemi kwayar maganin, ‘Paracetamol,’ na hadiya da fatan zan ji komai ya lafa. Amma ina sai ji nake rashin lafiyar ma karuwa take yi, bayan awa guda, sai na ji abin ya kara tsananta, nan take na nufi wajen yin bayangida, dubawan da zan yi, sai na ga duk dan kamfe na ya jike sharkaf da jini. 

Na yi mamakin hakan, domin kwanan nan na gama al’ada ta, nan na kara fahimtar cewa, lallai akwai matsala, ban kuwa bata lokaci ba, sai na sanya kaya na, na fita na tsare motar Tasi domin ta kai ni asibiti..”

Ma’aikaciyar Nas a asibitin, Northumbria Specialist Emergency Care Hospital, ita ta duba, Charlotte, da farko, kafin daga bisani ta kira wata na gaba da ita wacce take cikakkiyar Anguwar zoma. 

“Ko da su duka suka ce wai ina da ciki kuma ma wai haihuwa ce zan yi, sai na gaya masu, sam lallai ba hakan ba ne, domin ba yanda za a yi na haihu ba tare da na taba jin alama ba.” 

Bayan minti goma, suka sake gwadawa, suka tabbatar mani da cewa, tabbas ciki gareni dan watanni tara cifcif, sannan ma wai nakuda ce ta zo mani.

Charlotte, ta ce, “Ko da na ga da gaske ne suke yi, sai tsoro ya kara kama ni, na shiga cikin damuwar abin da zan shaidawa iyaye na, sannan kuma iyayen nawa me za su ce mani, idan haka kwatsam, suka ganni da jaririya da sunan diyata? Da misalin karfe 4:30 na asuba ne, wata ma’aikaciyar jinya a asibitin ta bugawa iyayen Charlotte, waya, mahaifiyar ta, Lynne Thomson, ‘yar shekaru 50, mai aikin share-share, da kuma, Bincent Thomson, shi ma mai shekaru 50, wanda yake shi injiniya ne, ta shaida masu cewa, ga fa diyar su ta zo haihuwa a asibiti. 

Farko iyayen nawa sun yi zaton ko dai na ga cikin ya shiga ne na wasu ‘yan makonni, na je domin na zubar da shi.

“Suna isowa, sai na ji na fashe da kuka, na kuma shaida masu cewa, ni ban taba zaton ina da ciki ba. Na yi mamaki, da na ga sun fahimce ni, sun kuma ba ni goyon baya da dukkanin taimako ba tare da nu na wata damuwa ba. Bayan sa’o’i, biyu ne da zuwa na asibitin na haifi Molly. 

Charlotte, ta ce, “Ina kuma haihuwan nata, sai na ji ina son ta, ga ta santaleliya shar, kalau cikin koshin lafiya, sai na ji kuma na shaku da ita.

Likitoci suka ce, ba ta sami kumburin ciki irin na masu ciki ne ba saboda yanayin jikinta, cikin nata ya shige sama ne wajen kirjinta. 

Charlotte, ta ce, abin kamar ba a, a ce wai a duk tsawon wannan lokacin ina da ciki, amma ni ban sani ba, wani kuma ma bai taba lura da hakan ba. Bayan kwanan su biyu a asibitin ne aka sallame su. 

Charlotte, ta ce, “Dukkanin kawaye da abokanai na, ba su yarda da ni ba, a lokacin da na rika gaya ma su cewa, na haihu, har sai da na nu na masu hoton Molly a matsayin diyata. 

Yanzun har na sanya Molly a makarantar Nursary, ni ma ina bakin aiki na.

Yanzun na rage zuwa wajen bukukuwa, kasantuwar ina da yarinyar da nake kulawa da ita. Ba wani abin da Molly za ta yi a rayuwarta ta ba ni mamaki, kamar mamakin da na ji na samunta da na yi da kuma haihuwanta.

Daga Jaridar Leadership

No comments:

Post a Comment