Jima’in Baki Na Jawo Mumunar Ciwon Sanyin Da Ke Da Wuyan Magani – Bincike


Hukumar Lafiya ta Duniya a binciken da ta yi a kasasshe 77 ta gano cewa jima’i ta baki yana jawo mummunan ciwon sanyi da ke yaduwa cikin sauri.
Hukumar ta yi gargadin cewa ciwon sanyin yana da wuyar magani ko kuma ma ba shi da magani kwata-kwata.
Cutar wadda ake kamuwa da ita ta hanyar saduwa tana bijirewa magani cikin sauri kuma tana shafar al’aura ce da uwar hanji da kuma makogwaron wanda ya ke fama da ita kamar yadda Dokta Teodora ta hukumar lafiya ta bayyana.
Ta ce, Idan mai fama da ciwon ya sha magani hakan ka iya jawo kwayoyin cutar Bacteria su kama makogwaro wadanda kuma suke bijire wa magani.
Ta ci gaba da cewa: “Idan aka yi amfani da magunguna wajen maganin ciwon makoshin hakan yana sa kwayoyin Bacteria su hadu da halittar Neisseria da ke makogwaro inda suke bijirewa magani.”
Masana sun yi gargadin cewa yanayin yana da ban tsoro saboda yadda ake kirkiro magunguna kadan don magance cutar.
Hukumar ta yi nazari ne a kasashe 77 wanda sakamakon binciken ya nuna cewa cutar tana bijirewa magunguna.
“An fara ganin matsalar kwayoyin cutar suna bijire wa magani ne a tsakannin wasu maza ‘yan luwadi a Amurka,” in Dokta Theodora.

No comments:

Post a Comment