Ban san yaya aka yi rayuwata ta susuce ba – Zainab Indomie


Fitacciyyar jarumar kannywood da ta yi fice a da can wanda aka fi sani da Zainab Indomie ta ce ba ta san yaya aka yi ba rayuwar aktin dinta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a masana’antar Kannywood.
Jarumar ta ce, ta samu daukaka tun tana karama a masana’antar fina-finan Hausa amma kaddara tasa a yanzu ta rasa komai, ba ta san abin da ya faru ba.
Ta ce, “Na samu daukaka tun ina karama a fina-finan Hausa, wani abu ya fau yanzu dai na rasa komai, babu ganganci a ciki, bana kuma ganin laifin kowa, ban kuma zargi kowa ba sakamakon mawuyacin halin dana shiga.”
“A halin yanzu ba zan iya tunawa da komai ba, ba zan iya cewa ga abin da ya sa na samu kaina a mawuyacin hali ba. Idan har laifi na ne ina rokon Allah ya yafe mini, Idan ma laifin wani ne to Allah ya yafe masa,” Inji ta
Ta ce, “Nagode wa Allah saboda jarrabawar da ya yi mini, Ina rokon Allah ya fitar da ni daga jarrabawar. Na mika kaina ga hannun Ubangiji.”
Jarumar ta roki Allah ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya