Jerin Jaruman Kannywood mata da suka fi Karbar kudi idan zasu fito a Fim


Jerin jarumai mata a masana'antar kannywood da suka fi sauran abokan sana'ar  su tsada idan har mutum na son su fito a fim din sa.

Wannan dai hasashe ne da muka yi tare kuma da bin kadin wasu sabbin fina-finan da jaruman suka yi a 'yan kwanakin nan. 

Duk da dai cewa jaruman kan rage kudin da suka caji akan wasu manyan furodusoshin da masu ruwa da tsaki a harkar watakila saboda mu'amalar da ke tsakanin su, wannan jerin sunayen an yi shi ne ba tare da la'akari da hakan ba.Rahama Sadau

Duk da dai cewa bata cika fitowa a fina-finan kannywood ba a yan kwanakin nan amma Rahama za'a iya cewa itace a sahun gaba wajen cajin kudi. 

Nafeesat Abdullahi

Itama duk da ba'a cika ganinta kamar da ba amma  hakan bai kashe mata kasuwa ba tana karbar kudade sosai indai har zata maka aiki.

 Hadiza Gabon

An taba jiyo wani forodusa ya mata lakani da " Ga aiki Sai tsada " wannan ne yake nuna cewa tana sahun gaba wajen  wawushe aljihun forodusoshi indai zata maka aiki.

Fati washa
Jarumar itama tana da tsada sosai ganin irin manyan finafinai da takeyi.

Haleema Atete
Jamila Nagudu
Aisha Tsamiya
Maryam Booth

Duka wadannan Jaruman suna firgita aljihun forodusoshi,  duk da cewa akwai sabbin Jarumai masu tasowa amman yanayin cajinsu bai kai wadannan ba.

@FimHausa.Com