Adam A. Zango Ya Saki Amaryarsa, Sallau Ya Saki Furera


Jaridar mujallar Fim ta wannan watan ta fito da sabbin labarai masu daukar hankulan jama'a musamman masoya fina-finan Hausa da bibiyar rayuwar jarumar masana'antar, babban labarin jaridar na wannan watan shine cewa, Adam A. Zango ya saki matarshi.


Jaridar ta kara wani dan jawabi akan wannan labari inda tace, shin ko Adamun zai maye gurbin tsohuwar matar tashi da daya daga cikin abokan aikinshi, Watau Fati Washa ko Zainab Indomie?

A baya dai bamu ji cewa ko akwai soyayya tsakanin Adam da Fati Washa ba amma akan Zainab Indomie, Adamu ya bayyana cewa babu soyayya tsakaninsu kawai dai yana taimaka matane ta dawo harkar fim.

Wani karin labari da ya dauki hankulan mutane a jaridar ta wannan watan shine me cewa, Sallau ya saki matarshi Furera, labarin yace Sallau din ya saki Furera bayan da ya gano sirrikanta, jaruman gudan biyu dai taurarine a wani shirin fim din Hausa na Dadin Kowa da ake nunawa a tashar Arewa24.

Kuma ba da dadewa bane Sallau din ya fito ya bayyana cewa matar tashi ta haifamai jariri.

Wani labari wanda tuni munji kishin-kishin dinshi shine na mutuwar auren tauraruwar fina-finan Hausa, Sa'adiya Kabala, watanni uku da yin auren, a labarin, tsohon mijin jarumar ya fadi dalilin da yasa ya sake ta.