Maryam Gidado ta fito da Sabon Salon Daukar Hoto


A makon da ya gabatane tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado ta dauki hoto inda ta dora kafarta daya a akan bayan mota, hoton ya jawo mata surutai inda da dama ke ganin cewa a matsayinta na mace be kamata tayi hakan ba. To da alama salon daukar hoton ya burge wasu daga cikin abokan sana'arta har sun fara kwaikwayarta.


A wannan hoton na sama, abokiyar aikintace me suna Hajara Isa ita ma ta dauki irin wannan hoto, Da kafa da ya akan mota.

Ko sauran 'yan matan gari zasu dauki wannan sabon salo kokuwa? Lokaci dai be bar komai ba.