Maza Matata Take Kawomin Cikin Gida, Shiyasa Na Saketa - Inji Mijin Sadiya Kabala


A makon da ya gabatane mujallar Fim Magazine ta tabbatar da mutuwar auren tauraruwar fina-finan Hausa, Sa'a diya kabala, bayan watanni uku da yin auren nata, kishin-kishin din mutuwar auren ya fara samuwane bayan da aka ga jarumar ta dawo da wallafa hotuna masu alamar tambaya a shafukanta na sada zumunta.

Mujallar ta ruwaito tsohon mijin jarumar inda ya bayyana cewa,dalilin da yasa ya sake ta shine tana kawo mishi maza gidane, wannan lamari ya dauki hankulan mutane inda wasu suka bayyana cewa ai dama duk wanda ya sai rariya ya san zatai zuba.

Wasu kuwa Allah wadai suka yi da mijin inda sukace be kamata ya fito Duniya yana tona manata asiri ba.

Source HutuDole.Com

No comments:

Post a Comment