Ali Nuhu Ya Samu Karramawa Na Digirin Digirgir Daga Kasar Togo


Fitaccen jarumi kuma sananne a masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya samu karramawa daga Jami’ar ISM Adonai da ke kasar Togo da digirin digirgir na girmamawa a kan kasuwanci da tallafawa matasa wato Entrepreneurship and Youth Development.
Wannan babban karramawar da Jarumin ya samu ba ya rasa nasaba da yadda sarki Ali Nuhu ya ke taimakawa matasa mata da maza ta hanyar sama musu aikin yi a masana’antar Kannywood ba tare da sun tsaya suna jiran aikin gwamnati ba.

No comments:

Post a Comment