Jarumi Ali Nuhu Yayi AsKi Mafi Tsada A KannyWood


Ali Nuhu, Sarki na daya daga cikin jigo a masana'antar fina-finan Hausa wanda ya bayar da gudummuwa matuka wajan ci gaban masana'antar, idan za'a kira sunayen taurarin masana'antar da suka fi yin fice tun kafuwarta to idan be zo a na daya ba, ba zai wuce na biyu ba.


A wannan karin wani tarihine da Alin ya kafa wanda ba'a taba samun wani jarumin masana'antar da irinshi ba.

Me shirya fina-finai, Alhaji Shehe na kan shirin wani sabon fim dinshi me suna Kazamin Shiri,  Ali Nuhu na daya daga cikin jaruman da zasu fito a wannan shiri to saidai ana bukatar ya aske gashin kanshi wanda watakila shi bashi da shirin yin hakan.

Amma Alhaji Sheshe ya janyo hankalin jarumin da makudan kudin da ya sakar mishi har 500,000 dandai kawai yayi wannan aski.

Sheshe ya saka wani hoton Ali Nuhu dake dauke da rubutun cewa, Aski mafi tsada a tarihin Kannywood furodusa Alhaji Sheshe ya biya Ali Nuhu naira 500,000 ya aske sumar sa don fitowa a shirin.

Lallai wannan abin tarihine wanda ba za'a taba mantawa dashi a masana'antar ba.

No comments:

Post a Comment