Ba Saboda Film Yasa Na Kashe Aurena Ba – Julaidiyya
Ba Saboda Film Bane Yasa Na Kashe Aurena Ba, Julaidiyya Gidan Badamasi Tayi Bayani Game Da Masu Cewa Ta Kashe Aurenta Ne Saboda Ta Shiga HarKar Fim.
Jarumar Kannywood mai suna Meera Shu’aibu wacce akafi sani da Junaidiyya a shirin Gidan Badamasi Ta bayyana dalilin fitowarta daga gidan mijin da kuma shigarta masana’antar Kannywood.
Junaidiyya, ta ce ba kamar yadda wasu ke yamaɗiɗi ba na cewa ta kashe aurenta ne domin ta shiga harkar fina-finai. Ta ce mutuwar aurenta bata da alaka da shigarta masana’antar.
Da ake tattaunawa da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na kafar BBC, Junaidiyya, tayi alfahari da ɗanta guda daya da take da shi, ta kuma ce bayan yin aurenta ta cire harkar Film a ranta.
To sai dai mutuwar aurenta ba jimawa taji sha’awar shiga masana’antar domin itama a dama da ita.
Ku kalli cikakkiyar tattaunawar da Junaidiyya tayi da sashen Hausa na BBC