Kannywood
Jaruman KannyWood Da A Koresu Saboda Bidiyon Tsiraici
Jerin Jaruman KannyWood Da A Koresu Sanadiyyar Bayyanar Bidiyo Ko Hotunan Tsiraicin Su A Duniya! Masana’antar KannyWood Matattara Ce Ta Mutane Da Dama. Cikinsu Akwai Maza Da Mata, Kuma Tsarin Masana’antar Shine Koyar Da Tarbiyya (A Yanda Suke Cewa)
Masana’antar Kuma Takanyi Kokari Domin Hukunta Duk Wani 6ata Gari Da Yazo Musu Da Wani Yanayi Ko Salo Na Rashin Tarbiyya Ko Makamancin Haka.
Akwai Wasu Jarumai Mata Da Masana’antar Ta Dauki Matakai Kansu, Na Koransu Daga Masana’antar Gaba Daya, Dalilin Bayyanar Hotuna Ko Bidiyon Tsiraicinsu. Jaruman Da Hakan Ya Kasance Dasu Yawanci Suna Kan Ganiyarsu Ne Sai Wani Akasi Ya Faru,
Jaruman Sun Hada Da Kubra Dako, Maryam Hiyana, A Baya Bayan Nan Kuma Akwai Safiyya Yusuf (Safara’u Kwana Casa’in)